Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Bellingham na Dortmund ya biya tarar Yuro dubu 40 saboda muzanta alkalin wasa

Hukumar kwallon kafar Jamus ta ci tarar dan wasan Ingila Jude Bellingham yuro dubu 40 bayan samunsa da laifin furta kalaman muzantawa kan alkalin wasa Felix Zwayer bayan hukunci a wasan da kungiyarsa Borussia Dortmund ta sha kaye hannun Bayern Munich da kwallaye 3 da 2.

Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham.
Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham. POOL/AFP
Talla

Hukumar ta ce kalaman da Bellingham mai shekaru 18 ya furta bai kamaci su fito daga bakin dan wasa ba, yayinda da ta bayyana tarar a matsayin ladabtarwa ga dan wasan tsakiyar na Ingila.

Tuni dai Borussia Dortmund ta sanar da cewa bata da shirin daukaka kara kan hukuncin da aka yankewa dan wasan nata.

Yayin wasan na ranar asabar dai Zwayer ya ki amincewa da bugun fenariti ga tawagar Dortmund amma kuma ya baiwa Munich makamanciyar damar, matakin da ya fusata Bellingham.

Dan wasan ya caccaki Zwayer ta hanyar diga ayar tambaya game da sahihancin aikinsa tare da kuma da gwada misali da yadda alkalin wasan ya samu kansa a wata almundahana cikin shekarar 2005 da ya kai ga dakatar da shi, yana mai cewa bazasu tsammaci adalci daga makamancin wannan alkali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.