Algeria na shirin ficewa daga gasar cin kofin Afrika tun a matakin rukuni
Tawagar Equatorial Guinea ta lallasa Algeria da kwallo 1 mai ban haushi a karawarsu ta jiya, nasarar da ta bar Algeriar mai rike da kambun gasar cike da fargabar yiwuwar iya ficewa daga gasar ta cin kofin Afrika tun daga matakin rukuni.
Wallafawa ranar:
Sai mintuna 20 na gab da karkare wasa ne Guinea ta zura kwallon ta hannun dam wasanta Esteban Obiang kuma Algeria ta gaza farkewa duk da bugun tazarar da ta samu ta hannun dan wasan Riyad Mahrez.
Har zuwa yanzu Algeria mai rike da kambun na gasar cin kofin Afrika na da maki 1 ne tal bayan tashi wasanta na farko babu kwallo tsakaninta da Sierra Leone, kuma matukar ta na bukatar tsallakewa zuwa mataki na gaba, dole ne ta yi nasara kan Ivory Coast.
Nasarar ta Equatorial Guinea kan Algeria ya kawo karshen wasanni 35 da kasar ta arewacin Afrika ta doka ba tare da anyi nasara akanta ba, wato dai shi ne shan kayen tawagar na farko tun bayan watan Oktoban 2018.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu