Isa ga babban shafi

Magoya baya na rige-rigen sayen tikitin wasan Najeriya da Portugal

Yayin da ya rage kwanaki uku gabanin wasan sada zumunci da tawagar Najeriya zata fafata Portugal a Lisbon, rahotanni na cewa magoya bayan sun kusa saye daukacin tikitin shiga filin wasa da aka tana da.

Wasu 'yan wasan tawagar super eagles ta Najeriya da zasu fafata wasan sada zumunta tsakaninta da Portugal. 15/15/22
Wasu 'yan wasan tawagar super eagles ta Najeriya da zasu fafata wasan sada zumunta tsakaninta da Portugal. 15/15/22 © NFF
Talla

A ranar Alhamis ne za a buga wasan sada zumunci tsakanin zakarun Afirka sau uku da kuma na Turai a shekarar 2016 a filin wasa na Estadio Jose Alvalade da ke Lisbon.

Shafin da ke daukar dawainiyar sayar ta tikitin Viagogo tuni ya sayar da kujeru dubu 45 cikin 49 da aka tanadarwa filin mai daukar mutane dubu 50,95.

Portugal za ta yi amfani da karawar a matsayin wani shiri na tunkarar gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar, yayin da Najeriya za ta yi fatan kawo karshen rashin nasara a har sau 12 da ta yi a wasannin sada zumunta na kasa da kasa adan tsakanin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.