Isa ga babban shafi

Yau ake kulle kasuwannin musayar 'yan wasan Turai ta bana

Yau talata ake rufe kasuwar musayar 'yan wasan kwallon kafa ta wannan kaka, inda Firimiyar Ingila ke kulle kasuwarta da misalin karfe 23:00 agogon GMT dai dai lokacin da bayanai ke nuna yiwuwar kudin da kungiyoyi suka kashe wajen cinikayyar 'yan wasan a bana ta iya zarta kowanne lokaci a tarihi.

Kammala cinikayyar 'yan wasan na nuna cewa za a koma wasanni gadan-gadan musamman wasannin gasar cin kofin zakarun Turai.
Kammala cinikayyar 'yan wasan na nuna cewa za a koma wasanni gadan-gadan musamman wasannin gasar cin kofin zakarun Turai. © AFP - ADRIAN DENNIS
Talla

Ya zuwa yanzu alkaluman. da aka tattara sun nuna yadda aka kashe tsabar kudin da yawansu ya kai fam miliyan 550 a wannan wata, wanda ya karya tarihin adadin fam miliyan 430 da kungiyoyin suka kashe a kakar wasa ta shekarar 2018. 

Firimiyar Ingila za ta kulle kasuwar da misalin karfe 11 yayinda Scotland ke shirin kullewa a da misalin karfe 23:59. 

Bayanai sun ce za a rufe kasuwar Bundesliga ta Jamus da karfe 17:00 sai Serie A ta Italiya da za a kulle da misalin karfe 19:00.

La Ligar Spain za ta kulle ta ta kasuwar da misalin karfe 23:00 yayinda Ligue 1 ta Faransa za ta kulle kasuwar ta da misalin karfe 11:59 duk dai a yau talata 31 ga watan Janairu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.