Isa ga babban shafi

Jude Bellingham na gab da komawa Real Madrid

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Borussian Dortmund Jude Bellingham, ya amince da tayin kwantiragin da Real Madrid ta yi masa. 

dan wasan Dortmund da Ingila Jude Bellingham kenan.
dan wasan Dortmund da Ingila Jude Bellingham kenan. POOL/AFP
Talla

Kwararre a bangaren cinikayyar ‘yan wasa Fabrizio Romano ya ce dan wasan ya yi farin ciki sosai da tayin da Madrid ta yi masa. 

Dama dai a makon da ya gabata ne aka ruwaito cewar, dan wasan tsakiyan dan asalin kasar Ingila, ya amince da cimma matsaya tsakanin sa da kungiyar. 

Kawo yanzu dai kungiyoyin basu cimma matsaya a tsakanin su gameda farashin dan wasan ba, duk da cewa kafin nan da karshen wannan wata ake saran kammala komai. 

Real Madrid dai ta dade ta na sanya ido akan dan wasan na tsakiya mai shekaru 19. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.