Isa ga babban shafi

Tauraruwar Harry Kane ta fara haskawa a gasar Bundesliga ta Jamus

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Ingila, Harry Kane ya zama dan wasan kasar na farko da ya iya nasarar zura kwallo a haskawarsa ta farko karkashin gasar Bundesliga ta Jamus.

Harry Kane na Ingila da ya koma Bayern Munich daga Tottenham.
Harry Kane na Ingila da ya koma Bayern Munich daga Tottenham. © Bayern Munich
Talla

Kane wanda ya koma Bayern Munich a wannan kaka, zuwa yanzu ya zura kwallaye a dukkanin wasanni biyu da ya doka wa kungiyar tun bayan komawarsa ciki har da nasararsu ta jiya kan FC Augsburg da ya zura kwallo har guda biyu.

Tun farko Bayern Munich ta samu kwallo a bagas ne biyo bayan kuskuren dan wasan Augsburg FC wato Auduokhai da ya zura kwallo a ragar kungiyarsa bisa kuskure a kokarinsa na kade farmakin da aka kai mata a minti na 32 da faro wasa.

Tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci Kane ya zura kwallo a minti na 40 yayin wani bugun fenariti da Munich ta samu yayinda ya kara wata kwallo ta daban a minti na 69 da taimakon Davies ko da ya ke Augsburg ta farke kwallo 1 a minti na 86 wanda ya sa aka tashi wasa 3 da 1.

Bayan tashhi daga wasan Kane ya wallafa wani sakon bidiyo a shafinsa na sada zumunta inda ya ke bayyana karawar ta jiya da kayataccciya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.