Isa ga babban shafi

Ronaldo ya zarta Messi, Neymar da Mbappe samun kudi a 2023

Cristiano Ronaldo ya yi wa abokin hamayyarsa Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe zarra, a matsayin dan wasan da ya fi kowa kudi a duniya cikin shekarar bana ta 2023.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo © LUSA - JOSE COELHO
Talla

Fitacciyar mujallar Forbes ta wallafa cewa Ronaldo ya samu kudaden da yawansu ya kai euro miliyan 211 a 2023, sama da abinda takwarorinsa fitattu suka samu.

A halin yanzu dai kusan euro miliyan 165 kwatankwacin dala miliyan 200 Ronaldo ke samu  a matsayin albashi daga kungiyarsa ta Al Nassr da ke gasar kwallon kafar Saudiya, bayan kulla yarjejeniya da ita a farkon shekarar bana.

Baya ga albashin da yake samu a duk shekara, Cristiano Ronaldo na kuma samun karin kudaden shigar da yawansu  ya kai euro miliyan 49, kwatankwacin dala miliyan 60 daga  tallace-tallace da sauran yarjeniyoyin da ya kulla da sauran manyan kamfanoni irinsu  na Nike da Jacon & Co a duk shekara.

Lionel Messi
Lionel Messi AP - Lynne Sladky

A bangaren Lionel Messi, kididdiga ta nuna cewar kudaden da dan wasan ya samu daga tsohuwar kungiyarsa ta Paris Saint-Germain da kuma Inter Miami da yake taka wa leda a yanzu, ya kai kusan dala miliyan 135 a duk shekara.

Neymar da Kylian Mbappé a kungiyar PSG
Neymar da Kylian Mbappé a kungiyar PSG © Christophe Ena/AP

‘Yan wasan da ke biye da Messi a matsayi na biyu da na uku su ne Neymar da Kylian Mbappe wadanda ke karbar dala miliyan 112 da kuma dala miliyan 110 a duk shekara.

Dan wasa na biyar mafi kudi a duniya shi ne Karim Benzema da ke samun albashin dala miliyan 106 a duk shekara, sai kuma Erling Haaland a matsayi na 6, wanda kuma shi ne mafi daukar albashi a gasar Firimiyar Ingila, inda yake daukar dala miliyan 58 a shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.