Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Fafaroma Benedict na "Sha Shida" ya jagoranci addu’oinsa na karshe

Fafaroma Benedict na “Sha Shida” ya jagoranci addu’oinsa na karshe, kafin ya sauka akan mukamin ranar Alhamis mai zuwa. Dubban mutane ne suka halarci fadar Vatican, inda Fafaroman ya shaida musu cewar Ubangiji ya bukace shi da ya hau tsauni dan cigaba da addu’oi. 

Fafaroma Benedict na "Sha Shida"
Fafaroma Benedict na "Sha Shida" REUTERS/Tony Gentile
Talla

“Ina mika sakon gaisuwa ga daukacin wadanda suka halarci wannan addu’a, idan Ubangiji na bukata na in aikata haka, ya zama wajibi na sadaukar da rain a.” Inji Fafaroma.

A farkon watan nan ne Fafaroman ya bayyana cewa zai yi murabus daga mukaminsa saboda yawan shekaru, wanda hakan abu ne da ba a taba gani ba a fadar ta Vatican a cikin shekaru 600 da suka shude.

Har ila yau wannan sanarwa, ta jawo cecekuce a tsakanin mabiya darikar Katolika a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.