Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka zata mayar da yan cin rani zuwa kasashensu na asali

A kokarin sa na kawo karshen kwarrarar bakin haure daga Mexico zuwa Amurka ,Shugaban kasar Donald Trump ya sanar da daukar matakin mayar da ilahirin yan cin rani da suka shigo kasar daga Mexico kasar su ta asali.Daukar matakin dake zuwa a dai dai lokacin da Shugaban kasar ke fatan samu amincewar Majalisa ga yukunrin sa na ware akala bilyan biyar na dala ,kudadden da za su taimaka wajen gina kantaga tsakanin Mexico da Amurka.

Donald Trump Shugaban Amurka na magana dangane da batun yan cin rani daga Mexico
Donald Trump Shugaban Amurka na magana dangane da batun yan cin rani daga Mexico REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

Ministocin cikin gida da mai kula da tsaron Amurka, sun tabbatar da cewa Amurka za ta mayar da baki yan cin rani da masu bukatar samun takardar zama daga Mexico zuwa kasar su ta asali.

Matakin zai shafar ga baki daya yan cin rani da suka shigo daga Mexico, a cewar Ministan cikin gidan Amurka, sabuwar gwamnatin Mexico na a sane da wannan mataki da kasar ta dau.

Wannan yukunri na Amurka na mayar da bakin zuwa mexico kasar su ta asali na a matsayin gaggarumar nasara a yaki da kwarrarar baki yan cin rani zuwa kasar ta Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kalubalanci matakin yan sanda da ya shafi salama biyo bayan kamen yan ci rani kamar dai yadda aka saba gani a Amurka, shugaba Trump ya bayyana cewa nan gaba kame da kora ne yan sanda zasu soma yi mudin aka capke yan cin rani .

Akalla an kiyasta yan cin rani milyan 10 da dubu da dari7 da suka shigo kasar .

Ta bakin wani jami’in diflomasiyar Mexico a Washington Jose Antonio Zabalgoitia, kasar sa za ta mutunta hakokin yan kasar tareda kare hakokin su ,ya kuma jaddada cewa Mexico ba zata bayar da mafaka zuwa bakin da aka kora daga Amurka mudin ba su shigar da bukatar haka a ba yaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.