Isa ga babban shafi
Turai

An fara gudanar da zaben ‘yan majalisu a Romania

A yau lahadi ake gudanar da zaben yan Majalisu a kasar Roumania duk da barrazanar cutar Covid 19 a wannan kasa.Gwamnatin kasar ta gargadi jama’a dangane da matakan kariya daga kamuwa da cutar.

Shugaban kasar Romania klaus iohannis
Shugaban kasar Romania klaus iohannis Daniel MIHAILESCU / AFP
Talla

Ana hasashen jama’a ba za su fito don kada kuri’ar su ba,bisa dalilan da suka shafi kiwon lafiya a wannan lokaci na Covid 19.

A jajubirin rufe yakin zabe, Shugaban kasar Klaus Iohannis ya bayyana fatan samun rinjaye a jam’iyyar sa ta PNL dake da kujerar Firaminista duk da cewa ta kasa samun rinjaye a baya.

Shugaban kasar na daukar alkawali gaban magoya bayan sa cewa indan ya samu rinjaye a wannan zaben na yau,tamkar sako ne ga yan adawa don ganin sun bar gwamnatin sa ta yiwa kasar aiki zuwa karshen wa’adin mulkin sa a shekara ta 2024.Sai dai yan adawa sun mayar da martani,inda suka dangata jam’iyyar Shugaban kasar a matsayi mai yiwa kudin tsarin mulki karen tsaye da kuma keta dokokin bil Adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.