Isa ga babban shafi
Romania

Mace ta farko Musulma za ta zama Friminista a Romania

Jam’iyyar Socialist a Romania na dab da zabar mace musulma ta farko a matsayin Friministar kasar.

Sevil Shhaideh na gab da zama mace kuma Musulma ta farko da ke rike mukamin Friminista a Romania
Sevil Shhaideh na gab da zama mace kuma Musulma ta farko da ke rike mukamin Friminista a Romania
Talla

Shugaban kasar Romanian Klaus Iohannis ya ce ranar lahadi mai zuwa zai nada Sevil Shhaideh a matsayin Friministar kasar.

Sanarwar da ke zuwa a dai-dai lokaci da al’ummar kasar ke mamaki, ganin cewa Shhaideh ba sananniya ba ce a fagen siysara kasar.

Shhaideh mai shekaru 52 a duniya ba ta, ta ba rike wani mukami a majalisar kasar ba. Sai dai a baya ta taba rike mukamin Ministar ma’aikatar raya yankuna na tsawon watanni shida.

Sevil Shhaideh kwararriya ce ta fuskar tattalin, kuma ta fito  ne daga al’ummar musulmi wanda 'yan tsirarru ne a kasar ta Romania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.