rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Zamfara BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya amince da Dala biliyan 1 don sayen makamai

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da ware Dala biliyan guda don sayen makaman yaki da ayyukan ta'addanci a Najeriya REUTERS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da bai wa ma’aikatar tsaron kasar Dala biliyan guda domin sayen sabbin makaman zamani da za ayi amfani da su wajen magance matsalar tsaron da ta addabi sassan kasar.


Ministan tsaro na kasar Janar Mansur Dan Ali ya sanar da haka bayan kammala taron Majalisar tsaron kasar da aka gudanar.

Ministan ya kuma bayyana girke karin jami’an tsaro a Jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina domin magance kalubalen tsarn a yankin.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani kazamin hari da kungiyar Boko Haram ta kai a jihar Borno a baya-bayan nan, in da ta kashe mutane akalla 20 tare da jikkata sama da 60 da kuma yadda 'yan bindiga ke kashe mutane babu kakkautawa a Zamfara.

A bangare guda, rahotanni daga Jihar Zamfara na cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar da suka addabi mutanen Jihar a wani artabu da suka yi a karamar hukumar Anka.

An ruwaito shugaban karamar hukumar Anka, Mustapha Gado Anka na cewar, sojojin sun yi nasarar hallaka ‘yan bindigar da dama, yayin da su ma sojojin suka rasa biyu daga cikin zaratan jami’ansu.

Gwamnatin Najeriya na fatan kawo karshen kisan gillar da ake samu a Zamfara bayan harin da ‘yan bindiga suka kai Bawar Daji wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane sama da 50.