Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya za ta wakilci Afrika a gasar kwallon yashi ta Duniya

Najeriya ta yi nasarar samun tikitin wakiltar nahiyar Afrika a gasar cin kofin duniya ta kwallon kan yashi da Paraguay za ta karbi bakunci a shekarar 2019.

Tawagar Najeriya ta kwallon kafar kan yashi, Supersand Eagles.
Tawagar Najeriya ta kwallon kafar kan yashi, Supersand Eagles. Ripples Nigeria
Talla

Tawagar Najeriya ta Supersand Eagles, ta samu nasarar ce a wasan kusa da na karshe na gasar kwallon kan yashin ta Afrika, bayan lallasa mai masaukin baki Masar da kwallaye 7-6.

Najeriya wadda karo na 6 kenan za ta halarci gasar kofin duniyar kwallon yashin a 2019, a yanzu za ta yi dakon wanda zai nasara a wasan kusa da na karshen da za’a fafata tsakanin Senegal mai rike da kofin gasar ta nahiyar Afrika da kuma Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.