Isa ga babban shafi
Iceland

Panama: Firimiyan Iceland ya yi murabus

Firaministan Iceland Sigmundur David Gunnlaugsson ya zamo mutum na farko da ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon tonon asirin da aka bankado a Panama, inda wasu takardun sirri suka nuna cewa shugabannin kasashe da attajirai har da ‘yan kasuwa na boye kadarorinsu a waje domin kaucewa biyan haraji da kuma halatta kudaden haram.  

Firaministan Iceland Sigmundur David Gunnlaugsson
Firaministan Iceland Sigmundur David Gunnlaugsson HALLDOR KOLBEINS / AFP
Talla

An bankado cewa Firaministan ya zuba jarin miliyoyan daloli tare matarsa a waje, matakin da ya durkusar da wasu bankunan Iceland a 2008.

Firaministan ya zamo na farko da ya ajiye mukaminsa na siyasa bayan bankado bayanan sirrin na Panama da ya ja hankulan kasashen duniya, inda aka binciki takardu daban daban har guda miliyan 11 da dubu 500 da ke nuna yadda wasu mutane masu karfin fada a ji suka yi huldar kudade a waje.

Kimanin ‘yan siyasan duniya 140 ne da suka hada da shgabannin kasashe aka ambata a cikin wannan badakala, amma wasu daga cikin su sun mayar da martani, tare da musanta aikata ba dai dai ba.

A bangare guda, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce, wannan al’amari na tonon silili ya nuna cewa kauracewa biyan haraji wata matsala ce da ta shafi duniya baki daya.

Firamniistan Pakistan, Nawas sheriff ya sanar da kafa wata hukumar shari’a domin binciken badakala wadda ta shafi ‘ya’yansa Hassan Nawaz da Hussain Nawaz.

Badakalar dai ta shafi shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin da dangin takwaransa na China Xi Jinping da kuma mahaifin Firaministan Birtaniya David Cameron da dan wasan kwallonn kafa Lionel Messi na Argentina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.