Isa ga babban shafi
Girka

Tattalin arzikin Girka ya farfado

Tattalin arzikin Kasar Girka da ke karkashin kulawar kungiyar Tarayyar Turai da hukumar bayar da lamani ta duniya IMF ya samu habaka a karon farko tun a 2014.

Tun a 2010 Girka ta fada cikin matsalar tattalin arziki
Tun a 2010 Girka ta fada cikin matsalar tattalin arziki REUTERS/Dado Ruvic/File Photo
Talla

Ma’aunin ci gaban tattalin arzikin ya karu da kashi 1.5 a watanni shida. Gwamnatin Girka ta bayyana fatar kara samun ci gaba kafin karshen 2016.

Girka na fatar kara samun bunkasar tattalin arzikin da kashi 2.7.

Tattalin arzikin Girka dai na kan hanyar farfadowa ne, sakamakon tsauraran matakan farfado da tattalin arziki da kungiyar Tarayyar Turai da hukumar bayar da lamani ta duniya IMF suka gindaya wa kasar.

IMF da Tarayyar Turai sun sanya wa Girka ido ne domin tabbatar da bin ka’idojin bashin da suka ba ta domin ganin ta ci gaba da kasancewa a jerin kasashen da ke amfani da kudin yuro a nahiyar turai, bayan ta fada cikin matsalar ta tattalin arziki a 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.