Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta samu Lagarde da laifi

Wata Kotun Faransa ta samu shugabar Hukumar Bada Lamuni ta duniya Christine Lagarde da laifin sakaci wajen biyan wani attajiri makudan kudade ta hanyar da ba ta kamata. 

Christine Lagarde, Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya IMF
Christine Lagarde, Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya IMF REUTERS/Charles Platiau
Talla

Lagarde ta bada umarnin biyan Bernad Tapei ne makudan kudaden da suka zarce Euro miliyan 400 a lokacin da ta ke rike da mukamin Ministan Kudin Faransa a shekarar 2008, bayan fitaccen dan kasuwar ya zargi bankin Credit Lyonnais mallakin gwamnati da yaudarar sa har ya karya farashin da ya siyar da kamfaninsa na adidas.

Duk da dai Kotun ta samu Lagarde da laifin, amma ba ta yanke mata wani takaman man hukunci ba, kuma an dauki matakin a kanta ne bayan ta wuce birnin Washington na Amurka daga Faransa.

Asusun IMF zai gudanar da zama na musamman don tattaunawa kan wannan batu, yayin da  Lagarde ta ce, ta dauki matakin biyan diyyar ce da kyakkayawar niyya, sabanin yadda wasu suka fassara, in da suke ganin ta yi haka ne saboda alakar da ke tsakanin Tapei da Nicolas Sarkozy da ke shugabantan Faransa a loakcin da lamarin ya faru.

Lauyan Lagarde ya ce, zai duba yiwuwar daukaka kara, yayin da kafafan yada labarann Faransa ke cewa, babu damar daukaka kara kan hukuncin da kotun shari’ar ta yanke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.