Isa ga babban shafi
Faransa

An bukaci Faransa ta canza salon matakan tsuke bakin aljihunta

Asusun bada lamuni na Duniya IMF yace akwai bukatar Faransa ta canza salon tafiyar da matakan tsuke bakin aljihunta domin farfado da tattalin arzikin kasar, a wani rahoto da hukumar ke fitarwa game da tattalin arzikin Faransa duk shekara.

Shugaban Asusun bada lamuni na Duniya Christine Lagarde
Shugaban Asusun bada lamuni na Duniya Christine Lagarde (REUTERS)
Talla

An bukaci kasar ta sake rage yawan kudaden da ta ke kashe wa ba tare da karin kudaden haraji ba.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Faransa ke kokarin daidaita gibin kasafin kudinta, kamar yadda shugaba Francois Hollande ke ikirarin bin tafarkin daidaita tattalin arzikin kasar.

Kodayake shugaban yace akwai bukatar karin haraji domin daidaita kasafin kudin Faransa.

A watan Yuni an samu karuwar rashin aikin yi a Faransa da kashi 11.2 wanda shi ne karo na 26 a jere da adadin ke karuwa.

Asusun Lamuni ya yi gargadin cewa za’a kammala shekarar 2013 Faransa na cikin komadar tattalin arziki inda ma’aunin karfin tattalin arzikin kasar zai kasance kasa da kashi 1. Amma akwai hasashen za’a iya samun kari a badi

Sai dai kuma Asusun Lamuni ya ba Faransa maki a fannin tsarin aikin yi domin ma’aikata a kasar suna da tabbas ga ayyukansu ba tare da wata barazana ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.