Isa ga babban shafi
Turkiya-Faransa

Turkiya ta kalubalanci matakin Faransa na tura soji Syria

Kasar Turkiya ta bayyana cewar shirin kasar Faransa na tura sojoji zuwa Syria zai zama mamayar kasar ce.Ministan tsaron Turkiya Nurettin Canikli yace muddin Faransa ta dauki aniyar tura dakarun ta zuwa Syria domin taimakawa Kurdawan dake Manbij, matakin zai yi karo da dokokin duniya.

Dakarun Turkiya a yankin Afrin
Dakarun Turkiya a yankin Afrin REUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Dangantaka tsakanin kasashen biyu tayi tsami jiya, sakamakon ganawar da shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayi da tawagar Kurdawa da kuma yan tawayen dake neman kauda shugaba Basahr al Assad daga karagar mulki.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na barazanar tura dakaru Manbij dake gabashin Afrin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.