rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

G7 G8 Rasha Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bamu da bukatar komawa cikin kasashen G7 - Rasha

media
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov. Reuters/Sergei Karpukhin

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa bata taba nema ko mika kokon barar mayar da ita cikin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 ba.


Lavrov ya bayyana haka yau Asabar, kwana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya nemi kasashen na G7 sun mai do da Rasha cikinsu gabannin taron su da aka fara jiya a kasar Canada.

A shekarar 2014, kasashen suka kori Rasha daga cikinsu, sakamakon mamaye yankin Crimea na kasar Ukraine da ta yi, inda suka koma kungiyar G7 daga G8 da suke a baya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce baki dayan kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 basu amince da dawowar Rasha cikinsu ba, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya bukata, gabannin taronsu a Canada wanda ya kawo karshe a yau Asabar.

Sai dai yayin da yake karin bayani kan matsayar ta su, shugaba Macron ya ce, akwai yi wuwar fara tattaunawa da kasar ta Rasha don duba yiwuwar janye korar da sukai mata.