rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Bakin-haure Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta yi watsi da hukuncin dauri saboda taimakawa bakin-haure

media
Wasu bakin-haure yayinda 'yan sanda ke kwashe su daga wani sansaninsu na wucin gadi dake birnin Paris. 30/5/2018. REUTERS/Benoit Tessier

Kotun daukaka kara a Faransa tayi watsi da hukuncin wata karamar kotu na daure wasu mutane biyu, saboda samun su da laifin taimakawa bakin-haure da suka shiga kasar ba tare da izini ba.


Da fari dai karamar kotun ta daure Cedric Herrou, wani manomi tsawon watanni 4 a gidan yari saboda taimakawa wasu baki 150 da suka shiga Faransa daga Italia, tare da wasu ‘yan kasar Eritrea 50 da ya baiwa mafaka.

Shi kuwa Pierre-Alain Mannoni an daure shi ne watanni biyu a gidan yari.

Alkalin kotun daukaka karar yace hukuncin ya sabawa halayyar Faransawa na taimakawa baki.