rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mexico

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rayuka sama da 70 sun salwanta a Mexico

media
Sojin kasar Mexico yayin sintiri a yankin Tlahuelilpan da aka samu fashewar butun mai da ya hallaka mutane 66. AP

Hukumomin kasar Mexico sun ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi lokacin dibar mai a wani bututu da ya fashe ya karu daga 66 zuwa 73.


Gwamnan Jihar Hidalgo, Omar Fayad, yace adadin ya karu ne bayan gano wasu karin gawarwaki 5, a gobarar da wasu mutane akalla 74 suka jikkata.

Wani faifan bidiyon da aka nada a wajen hadarin, ya nuna yadda mutane ke ci da wuta, yayin da wasu na gudu suna bukatar taimako.

Tuni shugaban kasa Andres Manual Lopez Obrador ya tafi yankin domin ganewa idan sa halin da ake ciki.