Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na sahun gaba wajen amfani da harsashin roba kan jama'a

Majalisar kare hakkin bil’adama ta Tarayyar Turai ta bukaci Faransa ta kawo karshen amfani da harsasan robar da ta ke yi kan jama’a a lokutan zanga-zanga ko wani hargitsi da nufin kwantar da tarzoma, inda kungiyar ta yi ikirarin cewa, dubban mutane sun jikkata a kasar sanadiyyar nau’in harsasan.

Wasu dandazon masu zanga-zanga kenan a birnin Paris na Faransa
Wasu dandazon masu zanga-zanga kenan a birnin Paris na Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Cikin sanarwar da Dunja Mijatovic babbar jami’ar Majalisar kare hakkin dan adama ta Tarayyar Turai ta fitar a yau, ta ce Faransa ita ce jagaba a jerin kasashen Turai da suka yi kaurin suna wajen amfani da nau’in harsasan robar kan jama’arsu musamman lokutan zanga-zanga.

Sanarwar ta ce akwai bukatar faransa ta daina amfani da nau’in harsasan robar wanda ta ke yiwa lakabi da LBD, la’akari da yadda ya ke illa ga jama’arta ciki kuwa harda wadanda ke makancewa sanadiyyar yadda harsashin ya same su aka.

Cikin sanarwar, Mijatovic ta ce duk da cewa jami’an tsaron Faransa za su yi amfani da tanadin doka wajen tabbatar da zaman lafiya, amma ya zama wajibi gwamnatin kasar ta sake nazari kan tanadin dokar kare lafiyar ‘yan kasa.

Sanarwar da majalisar kare hakkin dan adam ta Nahiyar Turai, ta buga misali da yadda jami’an tsaron kasar ta Faransa a baya-bayan suka rika amfani da harsasan na roba kan daruruwan masu zanga-zangar kasar wanda kuma ya kai ga jikkatar tarin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.