Isa ga babban shafi
spain

'yan sanda sun yi amfani da harsashin roba wajen tarwatsa 'yan Catalonia

Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Catalonia ta ce kimanin mutane 38 ne suka jikkata kawo yanzu bayan da jami’an ‘yansandan Spain su ka far musu, a kokarin da su ke na ganin sun hana su kada kuri’ar raba gardamar.

Jami'an 'Yan sanda a Spain na ci gaba da daukar matakin ganin al'ummar Catalonia ba su kada kuri'ar ballewa daga kasar ba.
Jami'an 'Yan sanda a Spain na ci gaba da daukar matakin ganin al'ummar Catalonia ba su kada kuri'ar ballewa daga kasar ba. Reuters
Talla

Jami’an ‘yansandan sun yi amfani da harsashin roba don tarwatsa taron masu zanga-zagar kin amincewa da matakin hana su kada kuri’ar raba gardamar ballewar yankin daga Spain.

Wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce yanzu haka ta sallami mutane 35 yayinda 3 da suka samu munanan raunuka ke ci gaba da karbar kulawa.

Wani Matashi Jon Marauri da shima ya fito don kada kuri’ar ya shaidawa Kamfanin dillacin Labaran Faransa cewa jami’an ‘yan sandan sun rika harba harsashin robar kan dandazon jama’ar da suka fito don kada kuri’ar.

Tun da safiyar yau ne dandazon masu kada kuri’a suka fito duk da hanin da gwamnatin Spain ta yin a cewa Kada kuri’ar ya sabawa ka’ida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.