Isa ga babban shafi
Spain

Yankin Catalonia ya bijirewa haramta zaben raba gardama

Dubban magoya bayan ganin ballewar yankin Catalonia daga kasar Spain, sun fara kada kuri’ar raba gardama don tabbatar da burinsu.

Jami'an 'yan sandan Spain, yayinda suke kokarin fasa wata kofar gilashi da aka sanyawa daya daga cikin rumfunan zaben da ake shirin kada kuria'ar raba gardama na neman ballewar yankin na Catalonia daga Spain.
Jami'an 'yan sandan Spain, yayinda suke kokarin fasa wata kofar gilashi da aka sanyawa daya daga cikin rumfunan zaben da ake shirin kada kuria'ar raba gardama na neman ballewar yankin na Catalonia daga Spain. REUTERS/Juan Medina
Talla

Sai dai a jami’an ‘yan sandan Spain sun kaddamar da samamen dakatar da kada kuri’ar, lamarin da ya haddasa arrangama tsakaninsu da wasu magoya bayan ballewar yankin na Catalonia.

Yayin kai samamen, ‘yan sandan, suna kwace baki dayan kayayyakin da suka tarar ne a rumfunan zaben.

Ko a jiya Asabar ‘yan sandan kasar sai da suka rufe rumfunan sama da 2000 a yankin na Catalonia.

Lamarin na zuwa bayanda shugabannin yankin Catalonia, ska sha alwashin gudanar da zaben raba garadamar neman ballewar yankin daga Spain, duk da haramta shi da gwamnatin kasar ta yi.

Rahotanni na cewa, tun a jiya a Asabar dubban mutanen yankin na Catalonia suka fara kafa layi a bakin makarantun da suka ayyana a matsayin rumfunan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.