Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta lalata manhajar da ta addabi komfutoci dubu 850

Wata tawagar kwararrun jami’an ‘yan sandan Faransa, ta yi nasarar lalata gurbatacciyar manhajar da ta addabi sama da kwamfutoci dubu 850 a sassan duniya.

Daya daga cikin jami'an tsaron Faransa masu lura da tsaron shafukan Intanet.
Daya daga cikin jami'an tsaron Faransa masu lura da tsaron shafukan Intanet. AFP/File
Talla

Faransa ce dai ke kula da tushen jerin kwamfutocin da ake kira Botnet, wadanda ake zaton masu kutse sun yi amfani da su wajen aiwatar da damfarar miliyoyin kudaden euro.

Hukumomin kasar ta Faransa sun bayyana cewa masu kutsen sun yi amfani da kwamfutocin na Botnet wajen lalata bayanan fiye da na’urorin na kwamfuta dubu 850 a sassa daban-daban na duniya.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron Faransar ta fitar ta bayyana cewa, masu kutsen sun yi nasara a ta’annatin na su, sai dai an yi kokarin dakatar da su ta hanyar mahadar kula da nau’rorin na Botnet da ke birnin Paris.

Tun da fari dai sashen kula da tsaron kwamfutoci na C3N a Faransar ne ya ankarar da mahukuntan kasar, game da yiwuwar kutsen, wanda kamfanin Avast mai dakile gurbatacciyar manhaja wato Virus ya gano.

Kamfanin na Avast ya bayyana yadda aka samu karuwar gurbatattun manhaja a kwanfutoci cikin fiye da kasashe 100 wanda kuma kai tsaye ake satar bayanai tare da damfarar jama’a.

Mahukuntan Faransar sun bayyana cewa lamarin yafi kamari a kasashen yankin tsakiya da kudancin nahiyar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.