Isa ga babban shafi
Faransa

Yajin aikin sufuri a Faransa ya shiga mako na 6

An shiga kwana na 37 da fara gudanar da yajin aikin sufuri mafi tsawo da aka gani a tarihin kasar Faransa a baya-bayan, lamarin da ya gurgunta harkokin sufuri a manyan biraren kasar da suka hada da Paris.Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin kwadagon kasar sun ci gaba da nuna adawa da shirin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron na yi wa dokar fansho gyarar fuska.

Masu yajin aikin a faransa na jerin gwano.
Masu yajin aikin a faransa na jerin gwano. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Manyan kungiyoyin kwadagon Faransa sun bukaci ma’aikatan jiragen kasa da na wutar lantarki da na jiragen ruwa da jami’an kiwon lafiya da malaman makarantu da lauyouyi da matuka jiragen sama da su shiga zanga-zangar ranar Alhamis.

Kawo yanzu layukan dogo guda biyu kacal daga ciki 14 ke aiki tukuru a birnin Paris, inda aka takaita zirga-zirgar sauran jiragen da wasu motocin jigilar fasinjoji.

Kamfanin jiragen kasa na kasa, SNCF ya takaita tashin nau’ukan jiragensa da dama, yayin da rarraba wutar lantarki ta yi kasa da kusan giggawatts bakwai a safiyar Alhamis a birnin Paris.

Babbar kungiyar kwadago ta CGT ta bukaci gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin gwamnatin Faransa na yi wa dokar fansho kwaskwarima, tana mai cewa za a ci gaba da boren har zuwa ranar Asabar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.