Isa ga babban shafi
Senegal

Senegal : Macky Sall ya yi wa fursunoni 500 afuwa

Shugaba Macky Sall na Senegal ya yi wa fursunoni kusan 500 afuwa domin ba su damar kasancewa a cikin iyalansu a sabuwar shekarar 2017. Amma Afuwar ba ta shafi wadanda aka samu da laifin zubar da jini ba da fataucin miyagun kwayoyi ko kuma wadanda aka sama da laifin gurbata al’adun jama’a ko addini.

Macky Sall, Shugaban kasar Sénégal.
Macky Sall, Shugaban kasar Sénégal. AFP PHOTO/SEYLLOU
Talla

A watan Yuli, lokacin bukukuwar sallar idi bayan Azumin watan Ramadan, shugaban kasar ya yi wa fursunoni 600 afuwa.

Irin wannan afuwar ce ta shafi Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade wanda aka saka a watan Yuni bayan zargin shi da azurta kan shi da kudaden al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.