Isa ga babban shafi
Najeriya-muhalli

Al'ummar Ogoni sun zargi sojin Najeriya da gurbata muhalli a yankin

Mazauna Yankin Naija Delta da ke Najeriya sun yi zargin cewar sojojin kasar da ke aikin hana masu fasa bututun mai na taimakawa wajen gurbata muhallin su ganin yadda aikin su ke kai ga fasa bututun da aka shimfida.

A cewar al'ummar yankin yadda sojin ke bankawa fetur din sata wuta yana taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhalli.
A cewar al'ummar yankin yadda sojin ke bankawa fetur din sata wuta yana taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhalli. News Nigeria
Talla

Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Faransa ya gudanar kan yadda ake gurbata muhallin yankunan da ke da arzikin man a Najeriya, ya nuna cewar masu satar mai su suka fi gurbata muhalli wajen fasa bututun da aka shimfida suna satar man domin sayarwa.

Sai dai binciken ya bayyana cewar suma kan su sojojin Najeriya da ke samar da tsaro a Yankin na taimakawa wajen fasa bututun wanda ke kai ga gurbata muhallin.

Gabriel Okoh, mazaunin Okpere da ke Jihar Delta, ya ce yanzu haka rayuwar su ta kasance cikin mawuyacin hali saboda yadda man ya lalata musu gonaki da ruwan sha da kuma kashe kifin da suke rayuwa akai.

Okoh ya ce yadda sojojin ke bankawa man sata da suka kama wuta baya taimaka musu wajen inganta muhallin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani gagarumin shiri na tsaftace yankin Ogoni irin sa na farko da wata gwamnati ta taba yi, sakamakon yadda kamfanonin man da suke aiki a Yankin suka lalata shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.