rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Najeriya Gabon

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Safarrar yara kanana daga kasashen yammacin Afrika zuwa Gabon

media
Wasu daga cikin yara dake gudanar da kananan ayyuka a Madagascar Melanie Stetson Freeman/The Christian Science Monitor via Getty

Lamarin safarrar yara kanana daga kasashen yammacin Afrika zuwa wasu kasashen nahiyar da suka hada da Gabon ya soma haifar da fargaba ga manyan kungiyoyin da ke kare hakokin bil adam a Afrika.


Hukumar Unicef ta samar da wani sashe a kasar ta Gabon da ke da hurumin bai wa wadanan yara mafaka, kafin daga bisali a dawo da su kasashen su na asali.

Hukumar ta bayyana cewa da dama daga cikin mutanen da ake tsallakawa da su zuwa Gabon na gudanar da kananan ayyuka da suka hada da gadi, tallace-tallace, yin jagora ga marasa gani da sauran su.

Akalla yara 80 ne hukumomin kasar suka tabbatar da ganowa da kuma ake kokarin dawo da su kasashensu na asali da suka hada da Najeriya, Benin, Togo da Nijar.