Hukumomin Gabon Sun Kori Ma'aikaciya Saboda Tuntuben Harshe
Hukumomi a kasar Gabon sun yi wa wata mai karanta labarai a tashan gidan Talabijin na kasar kokar kare daga aikin saboda tuntuben harshe a lokacin karanta labarai inda ta furta cewa Shugaban kasar Ali Bongo ya mutu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Dazun nan aka sanar da Koran ma'aikaciyar Wivien Ovandong saboda mummunar kuskure da ta aikata shekaranjiya Alhamis inda ta sanar da mutan kasar cewa Shugaban kasar ya mutu a Barcelona.
A zahiri dai shekaranjiya Alhamis ne aka yi bukin cika shekaru takwas da mutuwar Mahaifin Ali Bongo wato Omar Ali Bongo wanda yam utu a Barcelona a ranar 8 ga watan shida na shekara ta 2009 bayan kwashe shekaru kusan 40 yana bias madafun iko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu