Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta yankewa mutane 75 hukuncin kisa

Kotun Masar ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 75 ciki har da jagororin kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Brotherhood wadanda ake zargi da haddasa rikicin kasar na 2013 da ya kai ga kisan daruruwan jama’a.

Jami'an 'yan sandan kasar Masar, yayinda suke gadin mutanen da aka yankewa hukuncin kisa, wadanda ke tsare a bayan wata ragar kariya, a babbar kotun kasar da ke birnin Alkahira. 28, ga watan Yuli, 2018.
Jami'an 'yan sandan kasar Masar, yayinda suke gadin mutanen da aka yankewa hukuncin kisa, wadanda ke tsare a bayan wata ragar kariya, a babbar kotun kasar da ke birnin Alkahira. 28, ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Amr Abdallah Dalash
Talla

Mutanen 75, na daga cikin mutane 713 da hukumomin kasar suka kame wadanda ake zargi da kisan jami’an ‘yan sanda da kuma lalata wasu kadarorin gwamnati yayin rikicin na 2013, tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi.

A halin yanzu dai an mika hukuncin kisan da kotun ta yanke kan mutanen ga majalisar koli ta malaman kasar, wadda za ta tabbatar da zartas da hukuncin ko akasin haka.

Cikin wadanda ake yiwa shari’ar, akwai fitaccen dan jaridar Masar, Mahmud Abu Zeid, wanda aka fi sani da Shawkan, wanda ya karbi lambar girmamawa daga hukumar UNESCO a baya-bayan nan.

Sai dai kotun ta dage sauraren shari’ar dan jaridar, tare da wasu mutane 6 zuwa ranar da ba a kai ga bayyanawa ba.

Akalla mutane 700 suka mutu a rikicin Masar mai cike da tarihi wanda ya tashi a ranar 14 ga watan Agusta na 2013, ciki har da jami’an tsaro da wadanda basu ji ba basu gani ba, matakin da ya sa shugaban kasar mai ci Abdul Fatah Alsisi daukar matakin yanke hukuncin kisa kan wasu da ake zargi yayinda wasu kuma za su shafe shekaru a gidajen yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.