Isa ga babban shafi
Masar

An rantsar da Abdel Fattah al-Sisi a wani sabon wa'adi na biyu a Masar

Yau asabar aka rantsar da shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi wa’adi na biyu sakamakon lashe zaben da yayi da sama da kashi 97 a watan Maris.

Abdel Fattah Al Sisi Shugaban kasar Masar
Abdel Fattah Al Sisi Shugaban kasar Masar REUTERS
Talla

Shugaban ya sha rantsuwar ne a gaban yan Majalisun kasar inda ya jaddada aniyar sa na murkushe yan ta’addan da suka addabi Masar da kuma bunkasa tattalin arzikin ta.

Jiragen saman yaki sun yi ta shawagi dauke da tutar kasar, yayin da jiragen sama masu saukar ungulu suka mamaye sararin samaniyar birnin Alkahira.

Shugaba al Sisi wanda tsohon shugaban sojojin Masar ne, ya hambarar da gwamnatin shugaba Mohammed Morsi a shekarar 2013, yayin da ya tsaya zaben da ya lashe a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.