Isa ga babban shafi
Masar

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane 30 A Masar

Wata kotu a kasar Masar ta gabatar da bukatar Hukuncin kisa kan wasu mutane 30 da ake zargi suna da hannu a kisan wani Jami’i mai shigar da kara kotu cikin shekara ta 2015

Shugaba Abdel Fattah al-Sissi na kasar Masar
Shugaba Abdel Fattah al-Sissi na kasar Masar KHALED DESOUKI / AFP
Talla

Kotun ta tsaida ranar 22 ga watan gobe domin yanke hukunci na karshe bayan hukuncin farko na kisa da ta gabatar wa majalisar kula da harkokin addini ta kasar.

Marigayi mai shigar da karan Hisham Barakat hari da Bam aka kai masa yana cikin motarsa a birnin Cairo.

Gwamnatin kasar ta zargin kungiyoyi biyu da wannan kisa wadanda suka hada da kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi da kungiyar Hamas.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.