'Yan bindiga sun sace malamin jami'a a Kamaru
Wasu 'Yan bindiga a kasar Kamaru sun yi awon gaba da wani malamin jami’a a garin Beua da ke fama da tashin hankali tare da wani ma’aikacin jami’ar guda.
Wallafawa ranar:
Makarantar ta sanar da cewar an sace Farfesa Charles Doumta na sashen kimiyar lafiya ne tare da George Ongey da ke aiki a sashen bincike a cikin kwanaki 9 da suka gabata.
Mataimakin shugaban jami’ar, Ngomo Horace Manga ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na razana malamai da daliban jami’ar domin haifar da rudani wajen harkar bada ilimi.
Ita dai jami’ar ta Beau na dauke da dalibai akalla 12,000 a kasar ta Kamaru mai fama da rikice-rikice da ayyukan ta'addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu