rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Uganda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan sanda sun tarwatsa dandazon magoya bayan Bobi Wine a Uganda

media
Dan Majalisa Robert Kyagulanyi, da aka fi sani da Bobi Wayne a Uganda © AFP

'Yan sanda a Uganda sun harba hayaki mai sa hawaye tare da amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa magoya bayan Dan Majalisa Bobi Wine bayan sun yi wani gangami a wajen da ake saran ya gabatar da jawabi da kuma gudanar da bikin wakoki.


Yan Sanda sun dade suna arangama da dan majalisar kuma mawaki Bobi Wine saboda zargin da su ke masa na kin bin ka’ida wajen gudanar da tarukansa.

Kakakin Yan Sanda Patrick Oyango ya ce doka ta bai wa jami’an tsaro damar amfani da karfin da bai wuce kima ba, kuma abinda suka yi amfani da shi wajen tarwatsa taron kenan.

Rahotanni sun ce Yan Sanda sun kama dan majalisar, amma kuma Yan Sandan sun ce sun raka shi gida ne.