rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sudan ta buda sabon babin mulkin rikon kwaryar farar hula da soja

media
Ahmed al-Rabie, wakilin kungiyoyin farar hula ne a (D), sai Mohammed Hamdan Daglo, mataimaki na biyu na majalisar mulkin soja daga (H) a lokacin saka hannu kan yarjejeniyar da ta buda hanya ga soma mulkin Farar Hula a kasar 17/08/19. EBRAHIM HAMID / AFP

Kasar Sudan ta buda wani sabon babi a tarihin siyasr kasar na shimfida mulkin farar hula, bayan da ajiya Laraba aka rantsar da sabuwar majalisar tafiyar da mulkin rikon kwaryar kasar mai cikakken iko, wanda nadin Firayim Minista zai biyo wa baya nan gaba.


Wannan mataki dai ya maiye gurbin gwamnatin soji da ta rike ikon kasar bayan shafe watanni ana gudanar da zanga-zangar da ta kai sojoji suka tunbike daddaden shugaban kasar Omar al-bashir daga kan kujerar sa a watan Afrilun 2019

Sakamakon wannan rantsar da majaliar rikon kwaryar dai ya sa ya zama a karon farko da sudan ta fice daga karkashin ikon soji tun bayan juyin mulkin da ya kai Shugaba El-Bashir kan mulkin kasar a shekarar 1989

A yammacin jiya talata ne aka sanar da Sunaye 11 na shu’agabanin hadakar majalisar gamin gambizar mulkin farar hula da soji, bayan banbance banbancen ra’ayoyi da aka samu tsakanin yan adawa da janarorin sojin dake rike da mulkin.

An rantsar da Janar Abdel Fattah al-burhan wanda ke jagorantar majalisar mulkin soji a matsayin shugaban sabuwar majalisar kolin jagorancin mulkin rikon kwaryar na tsawon watanni 21 daga cikin 39 yayin wani daga cikin yan farar hular ya karasa sauran adadin watannin kamar yadda yarjejeniyar raba madafan iko ta farko ta tanada.