Bin Laden ya bar wasiyar kudi domin jihadi
Wasu bayanan sirri daga hukumomin Amurka sun ce jagoran kungiyar Al qa’ida Osama Bin Ladan, ya mallaki dukiya ta milyoyin daloli a kasar Sudan da ya tara tare da rubuta wasiyar ware kudaden domin taimakawa ayyukan jihadi.
Wallafawa ranar:
Hukumar tara bayanan sirrin Amurka ce ta bayyana hakan a shafinta Intanet.
An samu wasiyar ne daga cikin muhimman takardu da aka gano bayan kashe Bin Ladan a wani gidansa da yak e buya a Abbottabad na kasar Pakistan 2011.
Bin Laden ya rubuta wasiyar ne ta kudi da suka kai dala miliyan 29 cikin harshen larabci, mai dauke da sa hannun marigayin.
Sannan ya bukaci danginsa su bi umurnin shi wajen sarrafa kudaden ga ayyukan jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu