Isa ga babban shafi
Japan

Japan da Amurka na kokarin karfafa dangantaka

Firaministan Japan Shinzo Abe ya isa Hawaii domin ganawa da shugaba Barack Obama na Amurka, inda shugabannin biyu za su ziyarci barikin sojin ruwan Pearl Harbor na Amurka, wanda dakarun Japan suka kai wa hari da ya fusata Amurka ta shiga yakin duniya na biyu shekaru 75 da suka gabata.

Firaministan Japan Shinzo Abe, à Honolulu
Firaministan Japan Shinzo Abe, à Honolulu REUTERS/Hugh Gentry
Talla

Za a gudanar da wani bikin tunawa da sojojin Amurka dubu daya da 177 wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin sojin saman Japan shekarar 1941.

Wannan ne karon farko da wani Firaminista daga Japan ke ziyartar wannan barikin soji tun bayan kammala yakin duniya na biyu, kuma hakan na a matsayin alamar kara kyautatuwar alaka tsakanin kasashen biyu.

Kimanin watanni bakwai da suka gabata shugaba Barack Obama ya ziyarci Hiroshima da ke Japan, garin da harin bam na nukiliya ya narka a lokacin yakin duniya na biyu, kuma karon farko da wani shugaba na Amurka ya ziyarci garin.

Harin da dakarun Japan suka kai wa barikin sojin Pearl Harbor tare da kashe sojojin na Amurka dubu daya da 177, na a matsayin rashi mafi muni da ya faru da Amurka rana daya a lokacin yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.