Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Sai Jong-Un ya dawo hayyacinsa, inji Amurka

Amurka ta sha alwashin durkusar da Koriya ta Arewa ta hanyar karfafa wa kasar takunkumai har sai ta amince a hau teburin sulhu kan shirinta na makaman Nukiliya.

Shugaban Amurka Donald Trump da Kim Jong Un shugaban Koriya ta arewa
Shugaban Amurka Donald Trump da Kim Jong Un shugaban Koriya ta arewa Reuters / MANILA BULLETIN
Talla

Babban Kwamandan yankin Pacific na Amurka Admiral Harry Harris ya ce sun yi na’am da bukatar China da ta yi kiran hawa teburin sulhu domin kaucewa yaki tsakanin Washington da Pyongyang.

Sannan ya ce Amurka ba ta da nufin karya gwamnatin Kim Jung-Un illa fargar da shi ya dawo kan hayyacinsa. Sai dai kuma Kwamandan ya ce dukkan matakan da ya kamata a dauka Amurka za ta dauka.

Shugaba Donald Trump ya nanata wa jekadun kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa shi ne shugaban da zai yi maganin Koriya ta arewa tare da tabbatar da cewa Amurka na iya daukar matakin soji.

Sai dai kuma ga alamu Amurka ta karbi kiran da China ta yi na bin hanyoyin lalama da fahimtar juna domin kaucewa yaki tsakanin kasashen biyu.

Amma Koriya ta Arewa yanzu ta aikawa kasashen kudancin Asiya wasikar nemin goyon bayansu kan shirinta na shiga yaki da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.