Isa ga babban shafi
Italiya

Canjin Yanayi: Kasashen G7 sun yi alkawalin mutunta yarjejeniyar Paris

Mambobin kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya G7 sun yi alkawalin ci ci gaba da kokarin rage dumamar yanayi duk da takaddama da ke tsakaninsu da Amurka bayan Donald Trump ya yi watsi da yarjejeniyar Paris.

Taron kasashen G7 a Italiya
Taron kasashen G7 a Italiya REUTERS/Max Rossi
Talla

Ministan Muhalli na kasar Italia Gian Luca Galletti ya fadi a wajen taron kwana biyu na manyan kasashen 7 cewa yanzu duniya ta zura masu ido domin ganin yadda za a tunkari wannan al’amari na rage dumamar yanayi bayan ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar Paris.

Ya ce kungiyar G7 na da gagarumin rawar da za ta taka wajen ganin nasarar tsarin da aka dauko.

Scott Pruitt mutumin da shugaban Amurka Donald Trump ya nada don kula da Muhalli a kasar Amurka ya halarci taron amma kuma bai zauna an karkare taron da shi ba.

Ministan Muhalli na kasar Jamus Barbara Hendricks shi ma ya bar wajen taro kafin a kammala.

Patricia Espinosa, wakilin Majalisa Dinkin Duniya da ke kula da yarjejeniyar Paris dangane da rage dumamar yanayin, ya bayyana cewa ficewar Amurka daga cikinsu ba zai hana aiwatar da yarjejeniyar rage dumamar yanayi a duniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.