Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Rasha ta kori jakadun Amurka 755

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce, ya zama dole jami’an diflomasiyar Amurka har guda 755 su fice daga birnin Moscow a matsayin wani matakin ramako kan korar jakadun kasarsa da Amurkan ta yi a can baya.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin REUTERS/Sergei Savostyanov
Talla

Shugaba Putin ya kara da cewa, akwai yiwuwar gwamnatinsa ta kara daukan matakin kakaba takunkumi ga hukumomin Washington.

A wata hirar da ya yi da kafar talabijin ta Rasha, shugaba Putin ya ce, ya zuwa yanzu ma’aikatan diflomasiyar Amurka sama da dubu 1,000 ke aiki a ofisoshin jakadancin kasar da ke Rasha, saboda haka ya zama wajibi 755 su daina aikin da su ke yi domin komawa gida.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bukaci Amurka ta rage jami’anta zuwa 455 kamar yadda ita ma ta yi wa Rashan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.