Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya ki amincewa da yarjejeniyar nukiliyar Iran

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da matakinsa na kin tabbatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran tare da gargadin cewa a ko wane lokaci a yanzu kasarsa na iya watsi da yarjejeniyar.

Donald Trump ya ki tabbatar da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran da aka amince a 2015 zamanin Obama
Donald Trump ya ki tabbatar da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran da aka amince a 2015 zamanin Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Sai dai kuma nan take ne manyan kasashen Turai da Rasha da suka amince da yarjejeniyar tare Amurka da kuma Iran suka mayar wa Trump da martani.

Kamar yadda aka yi hasashe dai a cikin jawabinsa A Fadar White House, shugaba Donald Trump ya ki tabbatar da yarjejeniyar inda yanzu makomar yarjejeniyar ta koma a hannun majalisar Amurka.

“A yau Ina mai sanar da cewa ba za mu yi ba kuma ba zamu taba tabbatarwa ba”, inji Donald Trump.

A cikin jawabin Trump ya yi kakkausar suka ga Iran wacce ya danganta gwamnatin masu tsatstsauran ra’ayi kuma mai taimakawa ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Amma babbar jami’ar diflomasiyar Turai Federica Mogherini ta ce yarjejeniyar na aiki kuma domin Iran ta kiyaye sharuddan da aka amince.

Jami’ar ta ce Wannan wani tsari da aka tsara a aikace da suka shafi alkaluran nukiliya wanda kuma aka aiwatar, don haka shugaban Amurka na da karfin ikonsa amma ban da wannan.

A martaninsa, Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce matakin Trump ya tabbatar girman yadda yake kyamar Iraniyawa.

Yarjejeniyar da aka cim ma a 2015 ta kunshi a Iran ta dakatar da shirin mallakar makaman nukiliya inda a daya bangaren kuma manyan kasashen su janye takunkumai akanta.

Amma tun a yakin neman zabensa ne, shugaba Trump ke shan rantsuwar yin watsi da yarjeniyar wacce Amurka da Birtaniya da China da Faransa da Jamus da kuma Rasha da suka cim ma tsakaninsu da Iran a zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka Barack Obama.

Yarjejeniyar na cikin nasarorin da ake ganin Obama ya samu, wacce Trump kuma ya sha alwashin sokewa, duk da jami’an binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya sun ce Iran ta kiyaye sharuddan yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.