Isa ga babban shafi
UNESCO

UNESCO ta fitar da rahotonta na shekara kan ilimi

Hukumar bunkasa ilimi, kiimiya da kuma raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta fitar da rahotonta na shekarar 2017- 2018 kan ci gaban ilimi a kasashen duniya. Rahoton ya maida hankali kan yadda kasashen ke tallafa wa ci gaban ilimin yara ko akasin haka, in da ya ce, kalilan ne daga cikin kasashe masu tasowa ke bai wa shi’anin ilimi muhimmanci ga yaransu.

Har yanzu wasu kasashen Afrika na samun koma-baya a fannin ilimi
Har yanzu wasu kasashen Afrika na samun koma-baya a fannin ilimi REUTERS/Ryan Gray
Talla

Rahoton ba wai ya ta’allaka a kan kasashen nahiyar Afrika kawai ba ne, sai dai sakamakon kasashen ya nuna gazawa matuka ta wannan fanni na bunkasa ilimi ga yaransu.

Daya daga cikin batutuwan da rahoton ya ambata sun nuna cewa, a kasashen Afrika da ke kudu da sahara, wani bangare na yara dakikai ne ba su da ilimi ta yadda ba sa iya rubutu balantana su karanta, duk da cewa sun share tsawon shekaru a makaranta.

Wannan dai na zama abin takaici idan aka duba sakamakon wasu kasashen yankin sahel da suka hada da jamhuriyar Nijar ko kuma Chadi

UNESCO ta yada hotuna da dama game da rahoto ilimin yara a kasashen duniya

Haka kuma rahoton na UNESCO ya ce, daga cikin kasashen Afrika 13 da suka ware wa fannin karatun yara isassun kudade a kasafin kudinsu, sun hada da Mali, Burkinafaso da Cote d'Ivoire sakamakon karin da suka yi wa wannan fanni a kasafin kudinsu na 2010-2015.

Sai dai kuma kusan rabin dalibai 'yan makaratun share fagen shiga jami’a na watsar da karatun ne ba tare da samun damar kammala karatunsu ba.

Rahoton na UNESCO ya zana wasu kasashen Afrika da yara 'yan Firamari ke yin bankwana da karatu ba tare da kammala ta ba, ta farkosu kuma ita ce, Jamhuriyar Nijar da Chadi da Cote d'Ivoire da Congo  da Kamaru da Jamhuriyar Benin da Togo da Burkinafaso da Senegal da kuma Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.