rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila Bakin-haure Sudan Eritrea

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Isra'ila ta kaddamar da sabon shirin korar bakin-haure

media
Firminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu Ya ce kafin wannan lokacin sun kori bakin-haure 20000. REUTERS/Tsafrir Abayov/Pool

Gwamnatin Isra’ila ta ce zata biya kudade ga dubban bakin-haure ‘yan nahiyar Afrika da ke kasar ba bisa ka’ida ba, domin komawa zuwa kasashensu. Isra’ila ta yi tayin hade da barazanar daure dukkanin bakin-hauren da ta kama a kasar a karshen watan Maris.


A farkon wannan mako ne aka kaddamar da sabon tsarin biyan dala dubu 3,500 ga kowane daga cikin bakin Hauren, sai kuma sama musu tikitin jirgi kyauta zuwa kasashensu na ainahi ko kuma wasu kasashen, wadanda kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin dan adam suka ce ba za su wuce kasashen Rwanda da Uganda ba.

Mafi akasarin bakin-hauren da ke zaune a Isra’ila sun fito ne daga kasashen Eritrea da kuma Sudan, wadanda suka tsere daga azabtarwa da kuma rikicin da ake gwabzawa a yankunan da suka fito, sai kuma matsalar tattalin arziki.

Wani jami’in hukumar shige da fice na Israi’la da ya nemi a sakaya sunansa ya ce a halin da ake ciki, bakin-haure dubu 38,000 ne suka zaune a kasar ba bisa ka’ida ba, yayinda ake tsare da wasu dubu 1,420 a wasu manyan sansanoni biyu da aka tanada domin hakan.

Kafin wannan lokacin dai Firminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu Ya ce kafin wannan lokacin sun kori bakin-haure 20000.