rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Syria sun kai hari da makami mai guba

media
Harin da aka kaddamar a gabashin Ghouta da ke kusa da Damascus ya hallaka mutane da dama ABDULMONAM EASSA / AFP

Hare-haren sojin Syria da makami mai guba sun hallaka akalla mutane 30 a tungar ‘yan tawaye da ke kusa da birnin Damascus a jiya Litinin, yayin da al’ummar kasar ke ci gaba da shiga tsaka mai wuya sakamakon yakin shekaru bakwai da ya daidaita kasar.


Da dama daga cikin mazauna yankunan da ake gwabza yaki na korafi kan yadda lugudan-wuta ke tsananta, yayin da suke zargin sojin gwamnati da yin amfani da sinadari mai guba a yankunan da ke hannun ‘yan tawayen.

Amurka ta ce, akwai kwararan hujjoji game da amfani da sinadarin Chlorine a hare-haren da aka kadamar a ‘yan makwannin nan da suka hada da harin yankin Ghouta da ke kusa da Damascus.

Kungiyar da ke sanya ido kan hakkin bil’adama a Syria mai cibiya a Biraniya ta ce, an kai hare-haren sama da kuma na makaman atilari a gabashin Ghouta a ranar Litinin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen kimanin 30 tare da jikkata wasu gommai