Isa ga babban shafi
Birtaniya

Oxfam ta kori jami'anta bayan zargin cin zarafin mata

Kungiyar agaji ta Oxfam da ke Birtaniya ta fara daukar matakan kawo karshen cin zarafin mata ko lalata da su bayan zargin da ake kan jami’anta, ko da ya ke jami’in da ake zargin kan sa ya musanta. A cewar kungiyar za ta samar da wani kwamiti mai zaman kansa da zai tattara bayanai tare da tattaunawa da ma’aikatan don bankado gaskiyar batun dama kawo karshensa baya ga gindaya dokoki na musamman.

An Oxfam shop is seen, in London, Britain, February 11, 2018.
An Oxfam shop is seen, in London, Britain, February 11, 2018. © REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Babban daraktan kungiyar ta Oxfam Winnie Byanyima ya ce kofa a bude ta ke ga duk wanda ya taba fuskantar cin zarafi daga jami’an kungiyar kai tsaye ya isar da korafinsa, ta yadda kwamitin na su zai aiwatar da aikinsa don kwato musu hakkokinsu.

Kungiyar Oxfam ta shirya rubanya kudaden da take samarwa zuwa fiye da dala miliyan guda don bunkasa ayyukan jinkai, yayinda ta kara yawan jami’anta tare da karfafa shirin bayar da horo ga mabanbantan jinsi.

Sabon shirin kungiyar na zuwa ne mako guda bayan da aka zargi jami’anta da cin zarafin mata tare da tilasta musu karuwanci lokacin aikin bayar da agaji yayin girgizar kasar da ta faru a Haiti cikin shekarar 2010.

Tuni dai zargin ya tilastawa mataimakin babban daraktan kungiyar Penny Lawrence ajje aikinsa baya ga jakadun kungiyar uku a kasashen Afrika da suka hadar da Archbishop Desmond Tutu na Afrika ta kudu da kuma fitaccen mawakin nan Baaba Maal na Senegal sai kuma fitacciyar jaruma Minnie Driver.

A cewar shugaban kungiyar yanzu haka sun kori ma’aikata hudu baya ga tilastawa wasu 3 murabus din dole sakamon zargin na Haiti ko da yake dai daraktan Oxfam a Haiti lokacin faruwar lamarin Roland van Hauwermeiren, ya ki amincewa da zarge-zargen inda ya ce da kansa ya ke kin amincewa da tayin da mata ke masa akansu yayin aikinsa a Haitin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.