Isa ga babban shafi
China- Amurka

China za ta mayar wa Amurka da gagarumin martani

China ta bayyana kudirinta na mayar da gagarimin martani kan kasar Amurka ta hanyar kakaba haraji mai tsaurin kan kayan Amurka da ake shigar wa kasar. A cewar hukumomin China, matakin zai shafi waken soya da motoci da kuma kananan jiragen sama.

Shugaban China Xi Jinping da takwaransa na Amurka, Donald Trump
Shugaban China Xi Jinping da takwaransa na Amurka, Donald Trump REUTERS/Thomas Peter
Talla

Da fari dai Amurkan ce ta zargi Chinan da laifin satar fasahar kere-kere, abin da ya sa Amurkan ta sake lafta karin haraji kan kayayyakin kasar ta China da suka kai Dala biliyan 50, to sai dai hukumomin Beijing cikin hanzari suka mayar da martani.

Wannan yanayi na matakan karta-kwana da kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya ke dauka na haifar da gagarumin koma-baya a harkokin kasuwannin duniya da kasuwar musayar kudade.

Ko a jiya Laraba sai da aka fuskanci gagarumar faduwa a kasuwannin kasashen China da Hong-Kong da Korea ta Kudu, bayan da Chinan ta sanar da sabbin matakan, koda dai abin sai sambarka a kasashen Japan da Australia.

A cewar kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Geing Sheing, a shirye kasar ta ke ta shiga tattaunawa da Amurka, amma ya ce, an riga an bar kari tun ran tubani.

Masu sharhi dai na ganin bangarori da dama na tatalin arzikin duniya ka iya fuskantar koma-baya, muddin wadannan kasashe suka gaza cimma daidaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.