Faransa za ta bada tallafin yaki da Boko Haram a Najeriya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alkawarin bayar da tallafin Dalar Amurka miliyan 75 don ci gaba da yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Macron ya yi alkawarin ne a yayin ganawarsa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Abuja.
Macron wanda a karon farko kenan da yake ziyartar Najeriya a matsayin shugaban kasa, ya ce, gwamnatinsa za ta kuma bai wa Najeriyan bashin kudaden da yawansu ya kai Dala miliyan 475 don inganta harkokin sufuri a jihar Legas da samar da ruwan sha mai tsafta a jihar Kano, yayin da kuma za a bunkasa gandun dajin da ke jihar Ogun.
Gabanin ziyararsa a Najeriya, shugaba Macron ya gana da shugabannin kasashen Afrika a taron da suka gudanar a Mauritania, taron da ya mayar da hankali kan sha’anin tsaro a kasashen yankin Sahel da ke fama da rikicin Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu