Isa ga babban shafi

Macron zai jefi tsuntsu biyu da dutse daya a Rasha

Shugaban Faransa Emmnuel Macron, wanda ke Rasha domin karin karfin gwiwa ga tawagar kwallon kafa ta kasarsa,  zai gana da takwaransa na kasar Vladimir Putin kafin wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta bana.

Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. AFP
Talla

Ganawar shugabanin 2 za ta gudana ne kwana guda gabanin ganawar shugaban Amurka Donald Trump da Putin.

Kawo yanzu dai babu tabbacin ko shugabannin biyu za su gana ne a fadar Kremlin ko kuma za su hadu ne a filin wasan da Faransa za ta kara don neman kofin duniya a ranar Lahadi.

A bara dai shugabannin biyu sun karbi bakuncin juna a taruka daban-daban, inda dukkaninsu su ke da damuwa kusan iri daya musamman akan rikicin Syria.

Bayan ganawa da Emmanuel Macron na Faransa, shugaban na Rasha a ranar litinin zai gana da Donald Trump na Amurka a Helsinki, ganawar da ke matsayin ta farko tsakanin shugabannin biyu, wadda ake ganin ka iya kawo karshen tsamin alakar da ke tsakaninsu.

Manyan Jami’an Birtaniya dai sun kauracewa wasannin gasar cin kofin duniyar bana, sakamakon takaddamar da ta kunno kai watannin baya tsakanin Birtaniyar da Rasha kan zargin Rashan da yunkurin kisan tsohon jami’in liken asirinta kuma jami’in Birtaniya a yanzu.

Bayaga shugaba Macron akwai kuma ministan harkokin wajen Italiya da mataimakin Firaministan kasar Matteo Salvini da za su halarci wasan karshen na cin kofin duniya a Rasha.

Kafin yanzu dai an fuskancin takun-saka tsakanin Macron da Salvini game da matsalar ‘Yan cirani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.