Isa ga babban shafi

Trump ya yi barazanar soke ganawa da Putin

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar soke ganawar da ya tsara yi da shugaban Rasha Vladimir Putin a gefen taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da zai gudana a birnin Buones Aires na kasar Argentina a karshen wannan mako.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwansa na Rasha Vladimir Putin yayin wata ganawa Helsink a shekarar 2016
Shugaban Amurka Donald Trump da takwansa na Rasha Vladimir Putin yayin wata ganawa Helsink a shekarar 2016 Lehtikuva/Heikki Saukkomaa
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya sanya hannu kan dokar ta baci a lardunan da ke kan iyakar kasar da Rasha, sakamakon kama jirgin ruwan da dakarun Rasha suka yi a mashigin ruwan Azov.

Kafa dokar ta bacin har tsawon kwanaki 30 masu zuwa, wata alama ce da ke kara tabbatar da cewa alaka ta yi tsami sosai tsakanin Rasha da makociyarta Ukraine, wadanda suka jima suna takun-saka tun bayan ballewar yankin Cremea.

Da farko dai an tsara ganawa tsakanin Donald Trump ta Vladimir Putin a gefen taron kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki wato G20 a birnin Buenos Aires karshen wannan mako, to sai dai Trump ya yi barazanar soke ganawar.

Shugaba Putin a wannan laraba, ya ce matakin da dakarun kasar suka dauka na cafke jirgin ruwan kasar ta Ukraine ba inda ya saba wa doka, kuma yanzu haka mutane 24 da aka kama a wannan jrgi na cigaba da kasancewa a hannun mahukuntan kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.